MAIDANMANUDATAPROMAIDANMANUDATAPRO
Home
MAIDANMANU DATA PRO

Become an Agent

Zama Agent na MAIDANMANU DATA PRO

Agent prices

Farashin Agent mai rahusa

Your own customer panel

Panel na customers ɗinka

Reviewed and trusted

Ana tantancewa kafin a amince

How it works

  1. Read the Agent Terms and fill the form. New here? The same form opens your account.
  2. Applying is free for now.
  3. We review your application. Approved: your account becomes Agent.

Ka shiga account, ka karanta dokoki ka cika fom. A yanzu kyauta ne. Idan an amince, account ɗinka zai zama Agent.

Agent Terms / Dokokin Agent

  1. 1. No false promises or fake prices. Only quote the prices shown in the official App, website or bots.

    Babu alƙawarin ƙarya ko farashin bogi. Ka faɗi farashin da ke cikin App, website ko bot ɗinmu kawai.

  2. 2. Never collect customers' money into your personal account on our behalf. Customers pay only through the official App, website, bots or company account.

    Kada ka karɓi kuɗin customer a asusunka na kanka da sunan kamfani. Customer ya biya ta App, website, bot ko asusun kamfani kawai.

  3. 3. Never ask anyone for their PIN, password, OTP, BVN or NIN.

    Kada ka taɓa tambayar kowa PIN, password, OTP, BVN ko NIN ɗinsa.

  4. 4. No fake accounts, self-referrals or using other people's details to earn rewards.

    Babu buɗe account na bogi, referral na kanka, ko amfani da bayanan wasu don samun lada.

  5. 5. No spam, harassment or misleading adverts. Promote politely and respect people who say no.

    Babu spam, takura ko tallar yaudara. Ka yi talla cikin ladabi kuma ka girmama wanda ya ƙi.

  6. 6. You are not a staff member and cannot promise refunds. Send complaints to official support.

    Kai ba ma'aikacin kamfani ba ne, ba za ka yi alƙawarin refund ba. Ka tura ƙorafi zuwa official support.

  7. 7. Keep your customers' information private. Do not share or sell it.

    Ka kiyaye sirrin bayanan customers ɗinka. Kada ka yaɗa su ko ka sayar da su.

  8. 8. Use our name and logo only as provided. Do not create pages that pretend to be the official company.

    Ka yi amfani da sunanmu da logo kamar yadda muka bayar kawai. Kada ka buɗe shafi da ke nuna kai ne kamfanin.

  9. 9. Nothing illegal: no betting, fraud or resale of stolen airtime or data.

    Babu abin da ya saɓa doka: babu caca, zamba ko sayar da airtime ko data na sata.

  10. 10. We may review your activity and complaints at any time. Breaking any rule can lead to suspension, loss of Agent level and forfeited rewards.

    Za mu iya duba ayyukanka da ƙorafe-ƙorafe a kowane lokaci. Karya kowace doka na iya kai ga dakatarwa, cire matakin Agent da rasa lada.

  11. 11. You agree that your name, photo, location and Agent status are shown on your Agent ID card and on our public card-check page (maidanmanudatapro.com/verify-agent) so customers can confirm you are genuine. Your phone number, wallet, BVN and NIN are never shown.

    Ka amince a nuna sunanka, hotonka, wurinka da matsayinka na Agent a kan ID card ɗinka da kuma shafin tantance kati (maidanmanudatapro.com/verify-agent) domin customers su tabbatar kai na gaske ne. Ba za a taɓa nuna lambar wayarka, wallet, BVN ko NIN ɗinka ba.

  12. 12. Your Agent ID card is a company card, not a government ID, and does not make you a bank or POS agent. It is valid for 12 months and must be renewed; it remains company property and must be returned or stopped if your Agent status ends.

    ID card ɗin Agent katin kamfani ne, ba katin gwamnati ba, kuma ba ya nuna kai wakilin banki ko POS ne. Yana aiki na watanni 12 sannan a sabunta shi; mallakar kamfani ne kuma za a karɓe shi ko a dakatar da shi idan matsayinka na Agent ya ƙare.

  13. 13. Applying is free for now. If an Agent fee is introduced later, it will be charged from your wallet when you apply, refunded in full if we do not approve you, and not refundable once approved.

    A yanzu neman zama Agent kyauta ne. Idan an saka kuɗi nan gaba, za a cire su daga wallet lokacin da ka nema; idan ba mu amince ba za a mayar maka da su gaba ɗaya, idan an amince kuma ba a mayarwa.